8 Faburairu 2021 - 12:20
An Yi Kira Ga Al’ummar Kasar Libya Da Su Bai Wa Sabuwar Gwamnatin Kasar Hadin Kai

Wani memba na kungiyar malaman musulmi ta duniya, kuma dan kasar Libya Ali al-Salaby ne ya kira yi al’ummar kasar da su bai wa sabuwar gwamantin da aka zaba ta hanyar demokradiyya cikakken hadin kai domin ta yi aikinta kamar yadda ya dace.

ABNA24 : Al-Salaby ya kara da cewa; Abinda ya faru a birnin Geneva na zaben shugabannin kasar Libya bisa taimakon MDD, wata nasara ta aiki da hankali da kuma hikima, sannan kuma kawo karshen rikice-rikicen da aka yi ne a baya.

Har ila yau,memba din na kungiyar malaman musulunci ta duniya ya kuma yi kira ga sabbin shugabannin kasar ta Libya da su fadada fagen tattaunawa da suran bangarorin al’ummar ta kasar sannan kumasu tabbatarwa da duniya cewa za su iya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai aka zabi sabbin shugabannin kasar Libya ta hanyar kada kuri’a karkashin kulawar MDD a birnin Geneva.

342/